Albanian . Azərbaycani . العربية . Bengali . Bosanski . Burmese . 中文 . Czech . Danske . Deutsch . English . Française . Hausa . Hungarian . Indonesian . Italiano . Kyrgyz . Macedonian . Malay . Malayalam . Nederlandse . Norwegian . Pashto . Persian . Portuguese . Serbiana . Sindhi . Spanish . Svenska .Swahili . Thai . Türkçe . اردو

NASARA TA TABBATA A GWAGWARMAYAR ILIMI TA YAKI DA AKIDAR DARWINIYANCI

Me ya sa Darwiniyanci ya kasance barazana?


Charles Darwin

Darwiniyanci (Darwinism) akida ce ta maguzanci wadda ta dauki katari ko dace a matsayin addini. Darwiniyanci ya kasance mafi girman yaudara da karya da a ke yi da sunan ilimin kimiyya a duniya.

Duk wani ikrari da ‘yan akidar Darwiniyanci ke yi da sunan Labarin Asalin-halitta (evolution) karya ce tsagwaronta kawai.

Ba abin daya hada Labarin asalin-halitta da kimiyya.

Darwiniyanci addinin karya ne da a ka kirkira da nufin kautar da mutane da al’ummu daga yin imani da Allah (tabbas girman Allah ya wuce haka). Wannan mummunar akida babbar hanya ce ta bayyanar Dujal a karshen duniya.  Sannan saboda cewa al’umma ta gafala ga fahimtar haka, shi ya sa akidar ta ke samun galaba tana tunkuda mutane zuwa rayuwar kin addini, yaki, zalunci da kuma wahalar rayuwa. Darwiniyanci shine babban tushen duk wata akidar kin addini kamar zindikanci,  gurguzu da ra’ayin zahiranci (materialism). Darwiniyanci shine mabudin dukkan yakukuwa, ayyukan ta’adda, kisan kai, kisan kiyashi da sauran yanayin al’amura na ban tsoro da annoba da suke afkar da bala’i a cikin duniya. Darwiniyanci muguwar bakar hanya ce da Dujal ya dauka don ribatar mutane a kan tafarkinsa.

Kamar yadda Darwiniyawa ke riyawa a karairayinsu, wai mutum asalinsa dabba ne zalla; don haka a tunanin Darwiniyawa darajar kawai da za a baiwa mtum ba ta wuce ta dabba. Jigon akidar Darwiniyanci a dunkule shine cewa “mutum dabba ne wadda a daukacin rayuwarta cikin halin fada take.” Sakamakon haka ya haifar da akidar da ta doru a kan tsarin “rayuwar karfinka-ya-fisshe-ka” a tsakanin mutane. Don haka, wadanda suka riki wannan akida ta Darwiniyanci suka zama sababin bullowar akidu da ra’ayoyi irin su gurguzu da farkisanci (fascism  ) a fadin duniya inda suka yi sanadin jefa mutane cikin bala’I da wahala. Sama da mutane miliyan 250 suka rasa rayukansu lokacin yakin duniya na biyu wanda ya afku sakamakon tasirin ra’ayin ‘yan akidar Darwiniyanci da ta haifar ta hanyar akidun farkisanci da ta ‘yan Nazi, sannan kuma sama da mutane biliyan guda suka mutu ta hanyar danniyar siyasa wadda ta bijiro daga tsarin gurguzu, sa’annan yawan mutane marar adadi ne a ka karkashe su ta hanyar ta’addanci. Tushen wadannan akidu biyu kuwa ita ce akidar Darwiniyanci.

Ba bu tantama, duk wasu rigingimu da yakukuwa da ayyukan ta’addanci da yanzu suka game ko’ina a duniya, duk sun samo asalin su daga akidar Darwiniyanci. Wannan shine dalilin da ya sa akidar Darwiniyanci ta kasance wakiliyar ayyukan barna na Dujal da zai bayyana a karshen duniya nan ba da dadewa ba. Hanya daya kadai da imani zai rayu a bayan kasa, da kuma yadda za a kawo karshen wannan hali na ta’addanci da kuncin rayuwa shine ta hanyar ganin bayan addinin maguzanci na Darwiniyanci.

Ba bu tantama, duk wasu rigingimu da yakukuwa da ayyukan ta’addanci da yanzu suka game ko’ina a duniya,
duk sun samo asalin su daga akidar Darwiniyanci.

Wannan maguzancin addini ya ginu ne a kan tsantar yaudara da karya. Saboda haka kawo karshen wannan baudaddiyar akida, wato labarin Asalin-halitta kenan, to ba wani aiki ne mai wuya ba. Karni na 21 ya kasance lokacin da a ka fallasa tare da tona asirin wannan haramtacciya kuma mugunyar akida ta kowace fuska. Tabbas, kamar yadda a ke gani a wannan shafi na intanet, yayin da a ka fallasa karyar Labarin Asalin-halitta, to kuwa wannan addinin tatsuniya na Darwiniyanci, da ya rudu mutane a duniya kuma ya jawo wahalhalu da masifu, lokacin mutuwarsa ya yi.

Ubangijin 'yan ra'ayin Labarin Asalin Halitta na katari ko dace


Ganin yadda Adnan Oktar ya fallasa karairayi da tsabar haukar da ke cikin ra'ayin katari ko dace, yanzu kuma sai 'yan akidar Darwiniyanci ala dole suka daina amfani da kalmar "katari" kai tsaye a rubuce rubucen su.

A cewar masu ra'ayin Darwiniyanci, wai duk wani abin halitta mai ban al'ajabi a duniya ya samu ne kawai ta "KATARI" ko "DACE." Wai don kar su ce "Allah ne ya halicce su" (tabbas girman Allah ya wuce haka) sai suka dauki katari ko dace a matsayin ubangiji, a ganinsu, inda ido rufe suke danganta faruwar wadansu al'amura a matsayin su ne asalin samuwar wadannan madaukakan halittun Allah masu ban al'ajabi. Akidar Darwiniyanci ta yi galaba wajen rudar mutane da irin wannan shashashan dalili marar ma'ana. Irin yadda masana da ke da matsayin farfesa da ke koyarwa a jami'o'I, masana da malaman kimiyya wadanda suka yi zurfi a karatu da bincike, suke batun abubuwan da wai suka samu daga katari ko dace, wadanda abubuwa ne maraasa rai ko tunani, kai kace wasu abubuwa ne da ke da hankali da kwakwalwa da tunani wadanda kuma ke iya zartas da al'amari da kan su, ko kuwa cewa su ne tushen wadannan al'amura da muke gani na mu'ujizar Allah Mabuwayi (girman Allah ya wuce haka).

Katari ko dace shi ne ubangijin karya da Darwiniyawa suka rika, wanda suke ganin shi ne ya samar da halittar komai har kuma ya afkar da faruwar mu'ujizozi. A irin tosasshiyar kwakwalwar mabiya Darwiniyanci, lokaci da kuma katari ko dace, ta wata siga mai burgewa da daukar hankali, suke sanadin samuwar halittar komai a duniya. Wannan ra'ayi na hauka da rashin hankali yana riya cewar wai katari ko dace kan sabbaba abin da ya gagara yi ga bil-Adama, kuma cewa ta fuskar yana da sani (ko ilimi) hali da kuma dama da ta suka kere sanin masana kimiyya da kuma gwaje gwajensu baki daya. Ba shakka abu ne mai wuya ga duk mutum mai ilimi da tunani ya yarda da wannan shaci-fadin. A don haka ne ma ya sa dimbin rubuce rubucen da Adnan Oktar ya wallafa da nufin fallasa wa da kuma karyata karairayin da ke cikin labarin Asalin halitta, a cikin tsawon shekaru talatin, ba karamin tasiri ya yi ba wajen bude idon mutane inda suka gane cewa ashe labarin holokon ikrari ne kawai marar hujjar kamawa.

Ganin yadda Adnan Oktar ya fallasa karairayi da tsabar haukar da ke cikin ra'ayin katari ko dace, yanzu kuma sai 'yan akidar Darwiniyanci ala dole suka daina amfani da kalmar "katari" kai tsaye a rubuce rubucen su. A zaton su in suka fake da yin amfani da kalmomi makamantan waccan a ma'ana za su iya kaucewa kunyata da kuma karyatawa a idon duniya. To amma, ko su yi maganar katari, dace, ko gam-da-katar kai da ma kowace irin kalma mai ruwan haka, duk dai suna maganar al'amari ne wanda abubuwa marasa rai da tunani suka samar da kyakkyawar duniya mai rai da daidaito, da kyawun tsari wanda ya zarce kwaikwayo. Amma maimakon kare su daga abin kunya sai wadannan bayanai na shirme suka maida su ababen dariya da tausayi.

Darwiniya da ke kokarin bayyan yadda asalin rayuwa ta faro a duniya ta yin amfani da dalilai da hujjojin da suka sabawa hankali, DUK DA HAKA SUN KASA GABATAR DA GAMSASSHEN BAYANI KAN YADDA HATTA KWAYAR PROTEIN ZA TA IYA KIRKIRAR KANTA DA KANTA. Wannan ita ce muhimmiyar hujja ta farko da ya kamata a fahimta game da karairayin masu wannan akida. Tun da sun kasa yin bayanin yadda kwayar protein ta samu, sai suka shiga shirga karairayi don kare labarinsu. Duk wani labari ko hikaya da za su fada a kan samuwar rayuwa a doron kasa kirkirarre ne kawai marar tushe. Yadda gaskiya ta bayyana haka ta fito fili inda hujjoji suka bayyana daga miliyoyin kasusuwa na sassan abubuwa masu rai wadanda suka rayu tun daruruwan miliyoyin shekaru da suka wuce, haka na nuna karshen akidar Darwiniyanci ya zo kenan.

Kwararan Hujjoji Biyu kadai sun isa Rusa Labarin Asalin halitta

1-Kwayar protein daya tak ta rusa Labarin Asalin halitta

Darwiniyawa kan iya cika duniya da littattafai masu cike da karya da yaudara, su bijiro da kasusuwan tarihi birjik, su yi ta kushewa tare da karyata hujjojin kimiyya da ke gaskata al'amarin yin halitta yadda suke so, ko kuma su cika gari da fastoci masu hotunan ban mamaki, sannan su gabatar da su a matsayin hujjoji masu tabbatar da labarin Asalin halitta, amma sai dai hakan ba zai yi tasirin komai ba wajen hana kunyata su. Dalilin wannan kuwa shi ne cewa Darwiniyawa SUN KASA GABATAR DA GAMSASSHEN BAYANI KAN YADDA A KA SAMI KWAYAR PROTEIN DAYA TAK. Tsammanin kasancewar kwayar protein, wadda ita ce muhimmin tubalin ginin duk wani abu mai rai, cewa ta kirkiri kanta, abu ne marar yiwuwa; dalili kuwa shi ne ba a samun halittar kwayar protein daya tak har sai an sami dandazon protein kimanin dari kafin hakan ta faru. Ba sai mun zurfafa bayani kan wannan madaukakin tsari mai burgewa ba. Hujja daya kawai ta cewa kwayar protein guda daya ba ta iya samuwa in babu dandazon wasu protein din TA ISA RUSA RA'AYIN DARWINIYANCI. Amma irin kunyata da kayen da 'yan ra'ayin labarin Asalin halitta a kan al'amarin kwayar protein daya tak, ba karami ba ne.

Bugu da kari:

 • Ana bukatar DNA kafin a samar da protein
 • DNA ba zai samu ba sai da protein
 • Protein ba zai samu ba sai da DNA
 • Protein ba zai samu ba in babu protein
 • Protein ba zai samu ba in babu kowane daya daga cikin nau’in protein wadanda da su a ke kirkirar protein
 • Protein ba zai samu ba in babu ribosome
 • Protein ba zai samu ba sai da RNA
 • Protein ba zai samu ba sai da ATP
 • Protein ba zai samu ba in babu mitichondria da za ta samar da ATP
 • Protein ba zai samu ba in babu sinadarin ginin kwayar halitta (cell nucleus)
 • Protein ba zai samu ba in babu cytoplasm
 • Protein ba zai samu ba in babu tubalin ginin halitta na ‘organelle’ da ke cikin kwayar halitta
 • Kuma sai da protein ne dukkan tubalan ginin halitta na organelle da ke cikin kwayar halitta suke rayuwa da kuma motsi.
 • Ba za a sami protein ba in babu wadannan tubalan ginin halitta na organelle.

A dunkule dai:

ANA BUKATAR CIKAKKIYAR KWAYAR HALITTA KAFIN A SAMAR DA KWAYAR PROTEIN. IDAN BABU CIKAKKIYAR KWAYAR HALITTA, BA YADDA ZA A YI PROTEIN YA SAMU, da kyakkyawan tsarin halittarsa da a yau muke gani, wanda kuma sani da fahimtar mu a kan sa takaitacce ne. Sakamakon wadannan hujjoji ya sa tilas masu ra'ayin labarin Asalin halitta suka canja salo.

Daya daga cikin wadanda suka fara canja salon shi ne Richard Dawkins da shi da wasu Darwiniyawan irinsa inda suka fito da ikrarin wai "kwayar molecule ta kan ribanya kanta da kanta," wanda wannan tsantsar yaudara ce da rainin hankali. BA WATA KWAYAR MOLECULE A CIKIN KWAYAR HALITTA TA MUTUM DA TA KE DA IKON RIBANYA KANTA DA KANTA HAKA NAN BA TARE DA TAIMAKON WATA KWAYAR MOLECULE DIN BA.

Kamar yadda muka gani a sama, labarin Asalin halitta ya sha mummunan kaye tun daga farkon lamari. Yadda Darwiniyawa, wadanda suka rasa yadda za su yi da al'amarin kwayar protein daya tak, suke neman yaudara da rudar mutane a kan maganar nau'o'in abubuwa masu rai a doron kasa, shi ma babbar manuniya ce a kan tsantsar rudin da ke cikin labarin Asalin halitta.

 

2- Labarin Asalin Halitta ya sha kaye da hujjojin kasusuwan tarihi miliyan 350

Haka nan Darwiniyawa sun tafka karya da yaudara a kan batun kasusuwan tarihi. Su kan yiwa mutane rufa-ido da irin hotunan karya na yadda dabba take rikida daga wata halitta zuwa wata wanda suka kirkira suka zana da kansu. Su kan yi amfani da irin wadannan hotuna su yada karairayin akidarsu. Amma gaskiyar lamari shi ne har yau babu daya daga cikin 'yan ra'ayin labarin Asalin halitta da ya iya daga wani kashin tarihi ya ce "ga hujja daya da ke gaskata labarin Asalin halitta." Saboda ba su da hujjar yin hakan. ZANCEN RIKIDA DAGA WATA HALITTA ZUWA WATA KARYA NE.

Wannan hujjar ta girgiza mutanen da a ka wanke musu kwakwale da ra'ayin Darwiniyanci inda a tsawon shekaru ya yi tasiri a kansu ta hanyar rubuce rubucen 'yan akidar wanda koda yaushe suke ta babatun rikidewar halittar wai a matsayin hujjar labarin asalin halitta. Sai dai gaskiyar lamarin ita ce ba a taba samun ko da misalin guda na irin wannan yanayin rikidewar halitta ba. Wannan kuwa daya ce daga dimbin karairayi da rudun Darwiniyawa. Zuwa yau, an tono kasusuwan tarihi sama da miliyan 350. AMMA BABU DAYA DAGA CIKIN KASUSUWAN DA YA KE NUNA RIKIDEWAR HALITTA. Kowane guda daga cikin kasusuwan tarihin wadanda Darwiniyawan suka kafa hujja da su an gane karya ce kawai babu wanda ya nuna alamar rikidewar halitta. Mafi yawa daga cikin wadannan kasusuwan tarihi sama da miliyan 350 a gaskiya ma misalai ne na rayuwar miliyoyin shekaru da suka shude, sannan kuma har yau din nan irin nau'in halittarsu ne suke rayuwa. A takaice dai su ne suke rayuwa har yanzu. Abin da wannan yake nuna mana shi ne cewa abubuwa masu rai sun kasance a yadda suke a yanayin halitta tun tsawon miliyoyin shekaru, babu wani canji ko rikidewa daga wani nau'in halittar zuwa wani. Akwai wasu halittun da suka taba rayuwa, amma yanzu sun gushe babu irin su a duniya. Kasusuwan tarihi sun nuna mana yadda halitta da rayuwar abubuwa ta kasance mai ban al'ajabi da rikitarwa (ga mutum) tun a miliyoyin shekaru da suka shude. Wannan hujja ce kwakkwara ta bangaren kimiyya da ke karyata labarin Asalin halitta.

Yadda kasusuwan tarihi suka karyata labarin Asalin halitta shi ne al'amari na biyu da ya tumurmusa hancin akidar Darwiniyanci a kasa. Duk wani reshe ko sashe na kimiyya yana tabbatar da karyar labarin Asalin halitta. Duk wani binciken kimiyya yana karyata labarin Asalin halitta da karin hujjoji kwarara, a kowane irin hali da yanayi. To amma tunda yake wadannan hujjoji guda biyu da muka kawo a nan (wato rushewar labarin Asalin halitta da hujjojin kwayar protein da kuma ta kasusuwan tarihi) su kadai ma sun isa rugurguza wannan labari, babu bukatar mu kawo sauran tarin hujjojin da ke karyata labarin Asalin halitta. Wannan mummunan kaye ya isa kashe bakin tsanya, ya rufe bakin Darwiniyawa. Sannan kuma, a shafukan gaba za a tattauna muhimman al'amura da karin hujjoji musamman don maida martani ga ikrarin masu ra'ayin labarin Asalin halitta.

  KASUSUWAN TARIHIN NA ABUBUWA MASU RAI SUN KARYATA LABARIN ASALIN HALITTA (EVOLUTION)  
   
   
   
   
   
   
   
   
   
   
   
   
   
   


Shaci-fadi kan karyar Asalin halittar mutum shi ne Jigon akidar Darwiniyanci

Ra'ayin kama-karya na 'yan akidar Darwiniyanci wanda ke goyon bayan tsarin danniya da zalunci a duniya, kamar yadda muka yi bayani a nan, ta hanyar yin amfani da kafafen watsa labarai mallakarsu da kuma wadanda suke da tasiri a kan su inda suke ci gaba da yada tatsuniyar "Goggon biri-Mutum" da ke cewa asalin mutum biri ne. Amma sai ya kasance a kowane lokaci kasusuwan tarihin da a ke nunawa don kafa hujjar labarin Asalin halitta an tabbatar cewa kasusuwan biri ne da aka sani, don haka a nan a ka kashe bakin tsanya. Wannan sananniyar hanyar yaudara ce ta Darwiniyawa, inda wai don su kara tabbatar da kamanni da kuma dangantakar mutum da goggon biri, sun nuna goggon biri a matsayin wanda ya ke da dabi'u na mutum da kuma sauran al'amura irin su sarrafa na'ura da kuma yadda ya ke koyon darasi. Manufar su a nan ita ce don su yaudari mutane masu karancin sani kan halin su na karya da yaudara har su yarda cewa wai asalin mutum daga biri ne.

Koda yake tabbas, goggon biri da sauran birai suna da wasu kamannin halitta da suka yi kama da na mutum, to amma wannnan ba ya nufin cewa mutum da biri danginsu guda ba ne; halittu ne mabambanta. A bisa tsari da nufin Allah googon biri da sauran nau'o'in birai ba za su taba zama wani abu ba a tsawon rayuwarsu a duniya face halittarsu ta biri kawai. Duk irin nau'in horo ko kwarewar da za su samu hakan ba zai taba maida su mutane da ke yin tunani, kirdado, fahimta, hangen nesa da kuma yin aiki da ilimi, da iya yanke hukunci a kan lamari da kuma yin al'amura ko magana masu ma'ana cikin hayyaci ba. Duk wani kokari da kwarewar goggon biri ba za su taba kera jirgin sama ba, ko gina manyan gidaje masu benaye, ko rubuta wakoki ko kuma yin nazarin rayuwar mutane a dakunan gwaje gwajen kimiyya ba. Duk tsananin horon da suka samu ba za su iya fasaltawa ko tsara ayyuka ba, ko kuma su samar da al'umma wayayya mai ci gaba ta hanyar tsari da tunani. Dalilin haka kuwa shi ne cewa halitta irin ta biri halitta ce mai rai da ta kebanta da irin sigar halittar jikinta wadda Allah Mahalicci ya yi mata, amma kuma Allah bai yi mata baiwar hankali da lura da kuma ruhin tunani ba. Batun cewa suna iya yin wasu abubuwa da halayya irin na mutum, wannan ba zai zama hujja ta cewa wai biri shi ne kakan mutum ba.

Ruhin da Allah ya albarkaci mutum da shi shi ne ya maida shi mutum

Yayin da Darwiniyawa ke yin wannan ikrari, su na nufi ne su mantar da mu dangane da babban abin da ya bambanta mutane da birai. MUTUM ABU NE MAI RAI DA KE IYA FADIN "NI NE," WANDA YA SAN DA KASANCEWARSA ABIN HALITTA MAI RAI DA KUMA DALILIN HALITTARSA, WANDA KE IYA YIN TUNANI A KAN DALILIN RAYUWARSA A DUNIYA DA KUMA AL'AMARIN SAKAMAKO. MUTUM YANA DA RUHI. Saboda haka, mutum halitta ne mai rai wanda kuma ya sha bamban da sauran halittu masu rai. Banbancin halittar gangar jiki da na dabi'a, ba wani banbancin a-zo-a-gani ba ne in a ka kwatanta da ksancewar ruhi. IN HAR AKWAI WATA HALITTA MAI RAI DA TA KE DA RUHI, KO DA KUWA A ZAHIRIN HALITTA SUN BANBANTA DA MUTUM, TO WANNAN HALITTA ITA MA SUNAN TA MUTUM. Wannan shi ne babban abin da ya sa mutum ya zama mutum.

BABU WANI BAYANI DAGA MASU RA'AYIN ZAHIRANCI DA ZAI GAMSAR A KAN AL'AMARIN HALITTA MAI RAI, WANDA YA SAN KANSA, WANDA KE FADIN "NI NE." Babu wani labarin 'yan zahiranci da zai iya fayyace batun rikidaddiyar halitta da ta samu daga halitta mai rai wadda ba ta da kwakwalwa ko sanin yadda rayuwarta ta ke, sannan a ce ta haifar da halitta mai ruhi wadda ta ke da masaniya kan rayuwarta. Wannan shi ne abin da Darwiniyawa suke kaucewa, ba sa son yin magana a kai, kuma wannan shi ne ke tayar musu da hankali yayin da suke babatun asalin halittar mutum inda suke kokarin kafa hujja da wasu kokunan kai na karya da a ka tono. (http://darwinistsdilemma.com)

Saboda haka, duk wani ikrari da Darwiniyawa suke yadawa dangane da asalin halittar dan Adam karya ne. Da farko ma tukuna akwai jan aiki gaban Darwiniyawan na yin bayanin abin da ya maida mutum ya kasance mutum; ta yadda mutane suke tasirantuwa da abin da suka gani da kuma wanda suka ji da kunnuwansu, yadda suke tunani a kan haka, yin aiki da hankali, sannan ta yadda suke da wasu dabi'u irin su mutumta juna, soyayya da biyayya, da kuma yadda suke da ruhi wanda da shi ne suke fayyacewa su zartas da hukunci a kan al'amura. Amma har yau sun kasa bada gamsasshen bayani kan wannan al'amari, kuma abu ne mai wuya su iya yin hakan. Tabbas, asali da tushen samuwar rai da ruhi wanda shi ne banbancin mutum da sauran dabbobi, yana daga Allah. Allah ya yi wa mutum wannan baiwa ne daga gareshi inda da wannan ya bambanta mutum da sauran abubuwa masu rai. Hujjoji da bayanan Darwiniyawa a kan wannan al'amari rudu ne kawai da yaudara.

Allah yana fada a cikin Alkur'ani cewa Ya halicci mutum daga ruhinsa:

Shine wanda ya halicci dukkan abu ya kyautawa halittarsa. Kuma ya fari halittar mutum daga tabo; sa'annan ya fitar da 'ya'yansa daga wani ruwa wulakantacce; sannan ya suranta shi kuma ya hura masa daga ruhinsa; kuma ya sanya muku ji, da gani, da zukata. Godiyarku kadan ce! (Suratus Sajdah, aya ta 7-9)

 

Rikidar Halitta tana Kashe Rayuwa kuma ba za ta iya samar da sassan jiki wadanda ke iya aiki da juna ba

Darwiniyawa sun dage a kan ikrarinsu na wai dabbobi da sauran abubuwa masu rai sun samu ne sakamakon rikidar halitta bisa katari ko dace da kuma wai ita wannan makauniya rikida ta rashin tsari ita ce ta haifar da dukkan nau'in rayuwa da muke gani yanzu a bayan kasa.

Wannan ikrari yana cike da bayanan da suka saba wa hankali.

Rikida tana nufin karyewa, nakasa ko jirkicewar halittar sakamakon kudar zafi na "radiation" ko tasirin sinadarai a DNA da ke cikin tubalin ginin kwayar halitta wanda ya kunshi dukkan bayanan halittarsa. KASHI CASA'IN DA TARA NA DUKKAN RIKIDEWAR HALITTA SUNA KASHE WANNAN HALITTA (KO DABBA) inda kuma ragowar kashi dayan ba shi da tasiri ko kadan. BABU INDA A KA GANO CEWA RIKIDAR HALITTA TANA AMFANAR kowace irin halitta. Bugu da kari,

  *A ikrarin Darwiniyawa, rikidar halitta zai samar da sauyi ko canji na bai-daya da ya dace da kowane bangare na jiki.

  * Misali, kamar ikrarin ‘yan ra’ayin labarin Asalin halitta da ke nuna wai idan kunne ya fito a kuibin daman halitta mai rai sakamakon rikidar halitta irin wadda suke fada, saboda haka dole ne kuma wannan rikidar ta samar da wani kunnen a daya kuibin na hagu, wanda kuma yake dai dai da wancan dayan na dama. Duk wata sigar halitta ta kunne dole ya kasance ta bayyana a kowannensu.

  * Sabanin haka kuma za a sami babbar nakasa ko rashin daidaito, inda kuma sakamakon zai samar da wasu irin halittu masu juyayyun kunnuwa, barkalallun hakora, ko kuma a gansu da ido daya akan hanci dayan kuma a goshi. To amma tunda yake babu irin wannan nakasar daidaito a rayuwa, ikrarin Darwiniyawa yana nufi kenan waccan rikidar da suke magana dole ne ta samar da komai a mafi daidaito da kuma tsarin sifa.

  * Amma tunda yake cewa rikidar halitta kashi casa’in dinta hatsari ne da kuma cutarwa ga halittar sannan kuma kashi dayan ba shi da tasiri ko amfani, hakan ya sanya babu yadda za ta iya samar da sassan halitta masu tsari da daidaito da juna a lokaci guda.

  *Tasirin da rikidar halitta ke haifarwa a jikin halittu na asali shine kamar a harbe ta ne da bindga. Harbi kai tsaye a kan wata halitta zai halaka ta nan take. Koda a ce harsashi daya tak bai yi tasiri a kan dabbar ba ko kuma har ya iya kashe wata cuta da take jikin halittar, hakan ba zai canja wani abu ba. Tunda halittar ta riga ta halaka daga tasirin sauran harsashan guda casa’in da tara da suka shige jikinta.


  Ilmin Kimyya Abokin Gabar akidun Darwiniyanci da Zindikanci ne

  Labarin asalin haltta rudu ne da sunan kimiyya. Tsawon shekaru, Darwinyawa sun yi ta fakewa da sunan ilimin kimiyya suna batar da mutane akan labarin asalin halitta. Sai dai cewa ILIMIN KIMIYYA ABOKIN GABAR AKIDAR DARWINIYANCI NE. ILIMIN KIMIYYA MAKIYIN AKIDAR ZINDIKANCI NE. ILIMIN KIMYYA MAKIYIN KWAMINISANCI DA MARKSANCI NE. ILIMIN KIMIYYA NE MAKASHIN AKIDUN MARKISANCI, ZINDKANCI DA DARWINIYANCI. Ilimn kimiyya ne ya kawo karshen Darwiniyanci, shine ya tumurmusa hancin Darwiniyawa, ya rushe karairayinsu. Ilimin kimiyya shi ya rusa karyar masu ra'ayn labarin asalin halitta wadda suka shefe shekaru suna yaudarar mutane da ita. Ilimn kimyya shi ya tumbuke gishikin falsafar akidar Zindikanci. Ilimn kimiyya, har ila yau, shine ke fatattaka da kuma rushe Darwiniyanci a duk inda ya bulla. Saboda haka ilimin kimiyya shine BABBAR BARAZANA AKAN DARWINIYAWA.

  Ilmin kimiyya ne ya nuna cewa kwayoyin protein ba a samunsu bisa katari ko dace.

  Ilimin kimiyya ne ya bijiro da al’amarin ban mamaki game da rayuwar kwayar halitta (cell), kuma ya nuna cewa hakan ba zai taba faruwa bisa  katari ko dace ba.

  Ilimin kimiyya ne ya fito da gaskiyar cewa kasusuwan tarihi sama da miliyan 350 da a ka tono ba a ga alamun rikida a jikinsu ba.
  Ilimin kimiyya ne ya bayyanar da al’amura masu rikitar da kai a cikin halittar abubuwa masu rai sannan ya nuna cewa ba yadda za a yi wadannan halittu ace an same su ne ta hanyar abin da labarin asalin halitta ya bayyana.

  Ilimin kimyya ne ya nuna cewa babu yadda za a yi wata halitta mai rai ta rikide zuwa wata halittar.

  Ilimin kimyya ne ya bijiro da kasusuwan tarihi na zamanin Cambrian. Don haka, ilimin kimiyya shi kadai ya samar da hujjoji wadanda za su iya rushe labarin asalin halitta sannan kuma yana ci gaba da kawo wasu hujjojin. Ta yin amfani da kimiyya za ka ga gaba dayan ikrarin da Darwiniyawa ke yi ya rushe.

  ilimin kimiyya ya samar da hujjoji masu ba al’ajabi da suka yi fatali da shaci-fadin Darwiniyawa wadanda ke yaudarar mutane da cewa wai “labarin asalin halitta kimmiyya ne.” Ban da yiwa addini aiki da ilimn kimiyya ke yi, haka nan ya samar da hujjojin da ke tabbatar da samuwar Allah madaukaki. Don haka ilimin kimyya na wadanda suka yi imani da Allah ne, kuma abu ne mai amfani ga masu imani, ma’abota addini. Wannan hujja ta kasance babban abin bakin ciki ga Darwiniyawa a karni na  21.

  Allah ba ya jin kunyar buga misali – na sauro ko abin da ya fi shi kankanta. Amma wadanda suka yi imani, sun san cewa lalle gaskiya ce daga ubangijinsu. Amma wadanda suka kafirta za su ce“me Allah yake nufi da wannan misali?” Yana batar da masu yawa da shi kuma yana shiryar da masu yawa da shi. Kuma ba ya batarwa da shi sai fasikai. (Suratul Bakara, aya ta 26)

  Ya ku mutane! An buga misali, ku saurare shi. Wadanda ku ke kira sabanin Allah ba za su iya halittar kuda ba, ko da sun yi tarayya akan hakan. Kuma da kuda zai dauke wani abu daga wurinsu, ba za su iya karbo shi daga gareshi ba. Mabukaci da wanda ake bukata wurinsa duk sun raunana! (Suratul Hajji, aya ta 73)


  Ta yaya Akidar Darwiniyanci ta Mamaye Dunya?

  Akidar Darwinyanci yaudara ce da a ka gina ta a kan karya; toshewar tunani ne da duhun kai mutum ya yarda wai duk wani abu mai rai ya samu ne bisa katari ko dace. Sai dai kuma duk da yake cewa wannan akida ta sabawa dalilan hankali, sai gashi yaudararta ta mamaye dukkanin kasashen duniya; gwamnatocinsu, kananan makarantu da jami'o'i, cibiyoyin binciken kimyya, ma'aikatun gwamnati, kamfanonin jaridu da mujallu da gidajen rediyo da talbijin. Abin da ya kawo haka kuwa shine mummunar bakar aniya da kuma tsarin mulkin danniya, wadda dabi'a ce ta Darwiniyawa don ganin sun mallake duniya. Wannan bakar aniya da danniya, wanda suka shafe shekaru 150 suna aiwatarwa, yanzu ta fara sansanar kamshin mutuwa, koda yake har yanzu akwai sauran tasirinta.


  Michael Reisss, Daraktan sashen Ilimi a British Royal Academy ta Birtaniya, cikin gaggawa aka kore shi daga aikinsa saboda ya kawo shawarar sanya labarin Gaskiyar Halitta a manhajar karatu ta makarantu.

  Dakta Gvriel Avital, na Ma'aikatar Ilimi kuma Shugaban Sashen Kimiyya, an tsige shi daga aikinsa saboda rubuce rubuce da maganganunsa inda yake sanya alamar tambaya kan labarin asalin halitta.

  Babban jigon mulkin danniya na Darwinyawa ya ginu akan tursasawa, kama-karya, barazana da kuma zalunci. BA ZAKA TABA GANIN FARFESAN DA YA NUNA RASHIN YARDARSA DA LABARIN ASALIN HALITTA YANA KOYARWA a kusan kowace jami'a a duniya ba. BABU WANI SHUGABAN KASA DA ZAI IYA FITOWA FILI YA CE BAI YARDA DA RA'AYIN DARWINIYANCI BA. BABU WANI MALAMIN MAKARANTA DA ZAI IYA GAYAWA DALIBANSA CEWA LABARIN ASALIN HALITTA KARYA NE, HAKA KUMA DALIBAI BA ZA SU IYA BAYYANA WA MALAMANSU CEWA BA SU GASKATA LABARIN ASALIN HALITTA BA. Duk wani farfesa ko malamin makaranta da ya kuskura ya furta wannan to kuwa nan take za a raba shi da aikinsa ko aikinta. In kuma dalibi ne to zai fadi jarrabawa. ABU NE MAI WUYA KA GA AN BAR MINISTAN DA YA BAYYANA ADAWARSA GA AKIDAR ASALIN HALITTA A KAN MUKAMINSA NA GWAMNATI. Tabbas, kusan duk wani yunkuri a fadin duniya na ganin an sanya manhajar gaskiyar halitta cikin tsarin koyarwa tare da ta labarin asalin halitta a makarantu, HAR YANZU ABIN YA CI TURA.

  Sanannun kamfanonin jardu SUN RIKA DAUKAR RAHOTANNI akan kasusuwan tarihi na karya, kai ka ce sune hujjojin labarin asalin halitta. Sun taka rawarsu ce a wannan yaudar, don in ba su yi haka ba to harkar dab'insu tana cikin hatsari. Kuma abu mai wuya ga duk wani masanin kimiyya ko farfesa da ya riga ya rasa aikinsa saboda ya daukaka hujjojin ra'ayin gaskiyar halitta, ko kuma kawai don ya yi nuni da wata makala akan ra'ayin gaskiyar halitta, ya iya samun wani aikin ko mukamin da ya rasa. A bisa alamu ma, wannan mutum zai iya rasa da yawa daga cikin abokansa. Haka kuma, lalle abu ne mai kamar da wuya ya sake samun wani gurbi a fannin kimiyya kuma.

  SAURAN FAFESOSHIN DA AKA SAUKE DAGA AYYUKANSU SABODA SUNA GOYON BAYAN LABARIN GASKIYAR HALITTA
     
   

  Makamin da a ke amfani da shi shine tursasawa, kama-karya da kuma barazana. Saboda tsoratarwa da kuma kama-karya da tsarin danniya na Darwiniyawa ke amfani da shi, mutane sukan ji tsoron bayyana rashin amincewarsu da akidar Darwiniyanci, inda akan dole suke biyayya ga akidar har zuwa yau din nan. An kafa duk wasu matakai da a ke ganin za su hana yin tawaye ga Darwiniyanci. Ba don wannan ba, da mabiya wannan akida mai shigen tatsuniya ba su da sauran wata hujja da za su ci gaba da yada wannan ra'ayi na su marar tushe. Ana ta kururuta karya, sannan kuma wai laifi ne a karyata karyar! Labarin da a farkonsa aka yi ikrarin wai kimiyya ne, sai gashi an gane ashe maguzanci ne wanda ba abin da ya dangana shi da kimiyya, sannan don borin kunya ake tursasa mutane wai dole sai sun yi biyayya ga akidar da ba su amince ba. Abin lura ma anan shine yadda kiri kiri ba ko kunya ake kokarin dankarawa mutane akidar.

  Labarin asalin halitta, akidar da ta afkar da masifu a duniya, ita ce kuma ke neman dakile cigaban ilimin kimiyya

  A YAU ANA NARKAR DA MILIYOYIN DALOLI AKAN AYYUKAN BINCIKE DA DARUSSAN DA KE YADA LABARIN ASALIN HALITTA. Nazarin labarin asalin halitta na nufin kashe makudan kudade don a kirkiro sababbin karairayi a watsa su ta kafafen watsa labarai. A maimakon kashe wadannan kudade da aka ciro a jikin talakawa akan kirkira da yada karairayi, da za a iya amfani da shi a habaka fannonin binciken magunguna, misali a fannin warkar da ciwon sankara (cancer), ko ciwon Alzheimer, ko kuma a yi amfani da su don ceton rayukan miliyoyin mutane daga annobar fari a kasashen Afirka.

  Labarin asalin halitta, babbar karyar da aka shafe shekaru 150 ana yadawa a fadin duniya inda ake wanke kwakwalen mutane masu dimbin yawa ta hanyar amfani da makamin danniya na 'yan akidar Darwiniyanci, tana samun goyon baya a duniya ne ba wai don tana daga cikin ilimin kimiyya ba, sai saboda ana tursasawa da kuma wanke kwakwalensu don su gaskata ta yayin da tsarin mulkin danniya na Darwiniyanci ke bata kariya. Kada mutane su rudu don ganin kamar mafi yawan mutane suna biyayya ga wannan ra'ayi, saboda mafi yawan mutane ba su san cewa Darwiniyanci karya ce da yaudara ba, sannan kuma wasu suna nuna goyon bayansu ne don tsoron rasa ayyukansu ko kuma gudun suka da bi-ta-da-kulli. A yanzu haka mallakar dunya (ta fuskar juya tunanin mutane) da kuma duk wasu rubabbun ginshikan karya da yaudara da wannan TSARIN DANNIYA NA DARWINIYANCI, KUMA TSARIN SHAIDAN, ya kafa, an rusa su daya bayan daya. Da yardar Allah, rushewar gaba dayan akidar asalin halitta tana tafe nan ba da dadewa ba.


  Littafin "Atlas of Creation" (Taswirar Gaskiyar Halitta) da Darwiniyawan da suka dawo daga rakiyar akidarsu

  Idan aka gayawa mutumin da ke cikin daki a rufe cewa "akwai duhu a waje" akwai kyakkyawan zaton cewa zai gaskata hakan. Amma da zarar ya hango hasken rana ta wata 'yar kafa daga cikin dakin to babu yadda za a iya gamsar da shi cewa akwai duhu a waje.  Anne Brasseur, 'yar siyasa a Luxenbourg, ta gabatar da rahoto a hedikwatar Hukumar Raya Kasashen Turai a birnin Strasbourg, inda ta daga littafin Atlas of Creation sama tana nuna shi ga 'yan jaridun da suka taru a wurin tana fadin:

  "Harun Yahya musulmi ne, dan Turkiya,mai ra'ayin labarin gaskiyar halitta. Wannan littafi na farko kenan. Akwai wasu guda biyu. An watsa shi a kasashen turai cikin harsuna biyu, Turanci da Faransanci. Littafin yana cewa labarin asalin halitta karya ne, kuma Darwiniyanci shine tushen ta'addanci, kuma wai shine ya haddasa mulkin kama-marya na karni na 20 da sauransu…"

  To suma Darwiniyawa suna cikin irin wannan yanayi na rudani. Tsawon sama da shekaru 150 Darwiniyawa suna cin karensu ba babbaka, inda ko kunya babu suke yada karairayi da sunan kimiyya. Ba su taba jin kunyar karairayin da suke yi ba saboda suna da yakinin za su iya yaudarar mutane da wadannan rahotanni na karya. Sun yi ta nanatawa da kururuta karairayin na su ta hanyar hotuna da tsantsar dabarar juya tunani, inda hakan ya jawo musu gagarumar nasara da goyon baya. Amma kuma, yayin da abubuwa ke tafiya kamar yadda Darwiniyawa suka shirya, yayin da mutane ke ruduwa suna fadawa tarkon yaudararsu, yayin da kuma abu ya fara nisa har ta kai ana ganin laifi ne kin yarda da labarin asalin halitta, sai kawai ga haske ya bayya a idon mutane. Wannan haske kuwa shine littafin "Atlas of Creation" (Taswirar Gaskiyar Halitta).

  Yaduwar wannan lttafi a fadin duniya kamar wutar daji ta sanya cewa yanzu mutane da yawa ba wanda zai gaya musu akwai wai labarin asalin halitta su yarda. Babu mai ra'ayin Darwiniyanci daya da zai iya karyata dubban kasusuwan tarihi da aka bijiro a cikin littafin "Atlas of Creation." Bugu da kari kuma, kowane daya daga wadannan kasusuwa da wannan madaukakin littafi ya kawo, shi kadai ya isa ya rushe labarin asalin halitta.

  Bayyanar lttafin ta girgiza jaridu a Faransa, kasar da take daya daga cikin manyan cibiyoyin akidar Darwiniyanci a duniya, inda suka rika rubuta bayanai kamar haka: "Mummunar annoba a tarihin Faransa," "Annoba ta sauka daga sama" da kuma "Ginshiken wayewa da cigaban mu mai daruruwan shekaru ya rushe."

  Majalisar kasashen Turai mai ra'ayin Darwiniyanci ta dauki wannan madaukakin littafin a matsayin tarnaki wajen koyarda labarin asalin halitta a makarantu da jami'o'i, inda cikin firgici suka shiga kururuta al'amarin; daruruwan kafafen watsa labarai mallakar Darwiniyawa ala dole suka yada rahotannin irn gagarumin tasirin da "Atlas" ya haifar a fadin duniya.

  "Atlas of Creation" (Taswirar Halitta) ya taimaka wajen karfafa masu imani

  Bijirowar hujjoji da Adnan Oktar ya yi a fadin duniya na cewa ba a samun halittar kwayar protein guda daya ta hanyar katari ko dace, da kuma tabbatarwa da ya yi, da littafin "Atlas of Creation," cewa halittar miliyoyin abubuwa masu rai ba ta taba canjawa ba ko ta rikida, ita ce babbar hujja da ta tarwatsa karyar labarin asalin halitta a yau. Sakamakon wannan gagarumar nasara, a yanzu musulmin kwarai, kiristoci da kuma yahudawa sun sami damar gudanar da al'amuran addinansu cikin 'yanci da kuma yakini. Wasu ma'abota addini na gaskiya, wadanda a da suka rasa katabus da yakini saboda tasirin akidar Darwiniyanci, inda har ba sa iya gabatar da wasu al'amuran addini a fili, bayyanar wannan littafin ta kara musu karfin guiwa da yakini. Bayan fitowar wannan littafi da Adnan Oktar ya rubuta da kuma sauran ayyukansa masu daraja akan ganin bayan karyar labarin asalin halitta, NAN DA NAN SAI KOFA TA BUDE INDA A KE TA SHIRYA TARURRUKA DA BITOCI DON TONA ASIRIN LABARIN ASALIN HALITTA TARE DA KIRAN MUTANE DA SU YI IMANI DA DAYANTAKAR ALLAH A CIKIN SANSANONIN SOJAN AMERIKA, DA KUMA YADA WANNAN KIRA TA HANYAR RUBUTA "AKWAI ALLAH" A JIKIN MOTOCIN BAS (na haya) DA SUKE YAWO A TITUNAN BIRNIN LANDAN.

  A daidai lokacin da wadannan muhimman al'amura ke faruwa, an gabatar da TARURRUKAN BITOCI A KAN GASKIYAR HALITTA da dubban mutane suka halarta a kasashen Kanada, Amerika, Switzerland, Belgium, Jamus, Australia, da New Zealand, Faransa, Denmark, Sweden, Indonesia, Malaysia, Singapore, Dubai da kuma kasashe masu dama, yayin da gidajen talbijin da jaridu a fadin duniya suka bada labaran wadannan al'amura.

  Sakamakon wannan gagarumar nasara, sai nan da nan wasu daga cikin Darwinyiwa suka fara canja ra'ayi suna dawowa daga rakiyar tsohuwar akidarsu wadda ta fi kama da addinin maguzanci. Don kuwa karya ta kare musu; ba su kuma da abn da za su kare karya da rudin da suka shafe shekaru suna yi. AN YI TA RUFE MUJALLUN DARWINIYANCI DAYA BAYAN DAYA, BA KUMA DON RASHIN KUDI BA, SAI DON SU KANSU SUN DAWO DAGA BIN ABIN DA SUKE YADAWA, don haka suka rufe. Jaridu da mujallun Darwiniyawa, wadanda suka yi fice a duniya wajen yada rahotannin sababbin karairayi da aka kirkiro a kusan kowane mako, YANZU SUN KASA YADA KO DA GUDA DAYA. Karairayin Darwiniyawa, wadanda sune jigon akidar tasu, yanzu shiru ka ke ji sun kare. Darwiniyawa wadanda ba sa kasa a guiwa wajen kawo labarin asalin halitta a duk inda suka sami dama ta hanyar amfani da bayanai da hujjojin karya, yanzu tsit ba a jin kansu, sun yi shiru don kar su kara kunyata.

  Hotuna a jikin motocin bas bas na haya a Landan da ke tallata littafin Atlas of Creation. >>>

  TARURRUKAN LACCOCI AKAN HUJJOJIN GASKIYAR HALITTA D AKA YI DAGA AYYYUKAN ADNAN OKTAR SUN HAIFAR DA TASIRI A MANYAN BIRANE NA DUNIYA
  Switzerland- Lausanne >>> Switzerland- Lausanne >>>
  Jamus Luenen >>> Faransa Faris >>>
  Lambar yabon da a ka baiwa Adnan Oktar bayan taron laccar da aka yi a tashar jiragen sama ta San Antonio Airbase, a kasar Amerika.

  Kofar 'Yanto mutane Daga bala'in Akidar Darwiniyanci a bude Take

  Duk wasu addinan karya na tatsuniya yanzu haka sun fara shiga tasku da firgici da fuskantar rushewa a wannan zamani da muke ciki na karshen duniya, wanda kuma a cikinsa Hazrat Mahdi (as) da Annabi Isa (as) za su bayyana. Babu mai hanawa ko ya dakatar da rushewar su. Wannan tsari ne na Allah. Allah yana amfani da ayyukan Adnan Oktar a matsayin makaman da yake rusa tsarin karya da yaudara a wannan karni. Duk irin mutanen da suke bin akidar Darwiniyanci ido-rufe da sannu idanunsu za su bude su yi mamakin yadda aka rude su, yayin da su kuma Darwiniyawan za su yi nadamar tsarin karya da suka rika yiwa hidima suna kare shi. Duk da haka lokaci bai kure ba; sannan kuma ai amincewa da kuskuren da mutum ya aikata a baya da kuma rungumar gaskiya, hakan wata babbar baiwa ce da ke nuna tsarkin zuciya. Saboda haka, duk Darwiniyawan da suka fahimci illar wannan akida, to tabbas suna da dama da za su gyara barnar da suka shafe shekaru suna tafkawa, matukar dai suna nan da ransu a wannan duniya.